Kano: APC da NNPP sun bukaci magoya bayansu su tafi wajen tattara sakamako

0
116

Kwamitin Yakin Neman Zabe na Jam’iyyar APC a Kano ya bukaci magoya bayan jam’iyyar da su tafi wajen tattara sakamakon zabe na mazabu a fadin Jihar.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Kwamitin, Malam Muhammad Garba ya fitar, ya ce kiran na da muhimmanci don tabbatar da kuri’ar da aka kada ta yi tasiri.

Ita ma babbar jam’iyyar adawa ta NNPP a Jihar ta bukaci nata magoya bayan su fita don su tsare sakamakon.

A cikin wani sakon bidiyo da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar a zaben da ya gabata, Rabi’u Kwankwaso ya fitar da yammacin Asabar, ya ce suna da tabbacin samun nasara, amma duk da haka suna bukatar tsare sakamakon.

Ya ce sun samu wasu rahotannin sirri da ke nuna wasu na son yin amfani da wajen tattara sakamakon don tayar da zaune tsaye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here