APC ta sha kaye a gidan gwamnatin Kaduna

0
109

Jam’iyyar APC mai mulkin jihar Kaduna ta sha kaye a akwatunan zaɓe biyun da ke Gidan Sir Kashim Ibrahim, fadar gwamnatin jihar.

Ɗan takarar gwamna na PDP, Alhaji Isa Ashiru Kudan ne ya lashe akwati mai lamba 014 da ƙuri’u 77 yayinda ɗan takarar APC, Sanata Uba Sani ya samu ƙuri’u 40.

Jami’in zaɓe Mohammed Baso ya ce jam’iyyun PRP da NNPP sun samu ƙuri’u ɗai-ɗaya.

Haka ma akwatu mai lamba 013 PDP ta yi nasara da ƙuri’u 69 yayinda APC ta samu 64.

Jami’in zaɓe Kalu Kelechi Michael ya ce jam’iyyar LP ta samu takwas, yayinda PRP da NNPP suka samu ɗai-ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here