’Yan bindiga sun kashe mutum 3 a taron APC

0
99

Wasu ’yan bindiga sun tarwatsa taron jam’iyyar APC a unguwar Ile-Tuntun da ke Karamar hukumar Ibadan ta Kudu Maso Gabas a jihar Oyo, inda suka kashe mutum uku tare da lalata motoci da wasu kadarori.

Rahotanni sun ce an kai wa magoya bayan APC da dama hari.

Dan takarar majalisar wakilai na jam’iyyar a mazabar, Wariths Alawuje, ya sha da kyar a lokacin harin, kamar yadda ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho.

Ya ce: “Muna cikin wani taro da shugabannin jam’iyya lokacin muna jiran wasu ’yan jam’iyyar su karaso.

“Ba a dade ba sai muka ga wani babban dan jam’iyyar yana rada wa wani wata magana, sai muka fara jin karar harbe-harbe, kafin mu ankara, an ji wa da yawa daga cikin mutanenmu rauni, an lalata motoci, gidaje da ke kusa ba su tsira ba. Sun kashe wasu mutum uku.”

Kakakin ’yan sandan jihar, Adewale Osifeso, bai amsa waya ba bare a ji ta bakinsa kan faruwar lamarin.

Mutane da dama a jihar sun shiga fargaba kan faruwar tashe-tashen hankula gabanin zaben ranar Asabar.

Oyo na daya daga cikin jihohin da gwamna mai ci ke neman tazarce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here