Muna zargin NNPP na shirya magudi a zaben gwamna – Gwamnatin Kano

0
109

Gwamnatin Jihar Kano na zargin jam’iyyar adawa ta NNPP da shirin amfani da jami’an sa ido na bogi da nufin yin magudi a zaben gwamna da ’yan majalisar dokokin jiha da za a gudanar ranar Asabar.

Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba, ya yi zargin cewa NNPP ta buga takardun sa ido kan zabe an bogi ga jami’an bogi sama da 150 da take shirin turawa rumfunan zabe a birnin Kano ranar Asabar.

Ya yi zargin cewa NNPP ta yi hakan ne da nufin ba wa jami’an bogi damar kaiwa ga muhimman abubuwa a cibiyoyin zabe domin samun damar yin magudi da kuma sayen kuri’a.

Don haka ya bukaci jama’a sa kai karar duk wanda suka gani da katin sa ido kan zabe da bogi ga jami’an tsaro, yana mai kira kuma ga jami’an tsaron da su dauki matakin da ya dace a kan sojojin gonar.

Jam’iyyar dai ba ta mayar da martani kan zargin ba tukuna, amma a baya-bayan nan gwamnatin APC ta Jihar Kano da NNPP na yawan zargin juna da shirya magudi ko rikici a zaben da ke tafe.

Wannan dambarwa ta kai ga sauya Kwamishinonin ’Yan Sanda da aka tura Jihar Kano sau akalla biyar cikin dan kankanin lokaci.

A lokua daban-daban APC da NNPP na zargin wasu daga cikin kwamishinonin ’yan sandan da shiga harkokin siyasa ko kuma rashin daukar matakin da ya dace kama masu neman kawo rikici.

A ranar Alhamis NNPP ta gudanar da zanga-zangar neman a cire Daraktan hukumar tsaro ta DSS na Jihar Kano, bisa zarginsa da alaka da Gwamna Abdullahi Ganduje.

Jam’iyyar na zargin Daraktan DSS na Kano, Ganduje ne ya bukaci a kai shi jihar, kuma sama da shekara daya yanzu da lokacinsa na ritaya ya yi, amma ya ci gaba da, matakin da take zargin shiri ne na amfani da shi domin murde zabe.

A ranar ce kuma DSS ta tsare wasu magoya bayan NNPP biyu bisa zargin tunzura jama’a gabanin zaben da ke tafe.

Hukumar ta gurfanar da wadanda ake zargin a kotu, kuma ta samu izinin ci gaba da tsare su na mako guda, sai bayan zaben.

NNPP dai ta bukaci a sako mambobin nata.

A baya dai dan takarar Gwamnan Kano a NNPP, Abba Kabir Yusuf, da matar shugaban DSS, sun samu sa-in-sa a filin jirgi na Malam Aminu Kano.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here