Mun rasa mutum 5 a arangama da ayarin gwamnan Kaduna -‘Yan Shi’a

0
98

Mabiya darikar shi’a ta kasa ta yi ikirarin cewa, mabiya kungiyar biyar ne suka rasa rayukansu, inda wasu da dama suka samu raunuka biyo bayan arangamar da suka da yi ayarin motocin gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a ranar Alhamis.

Daya daga cikin jagororin darikar, Sheikh Aliyu Umar ne, ya shaida wa manema cewar arangamar ta auku ne a karamar hukumar Igabi a jihar.

Ya sanar da cewa, kungiyar za ta maka gwamnatin jihar a gaban kotu saboda kashe mata ‘ya’yanta, inda ya ce, arangamar ta auku ne a yayin da ‘ya’yan kungiyar ke kan gudanar da muzahara cikin kwanciyar hankali don bukatar a sakar wa shugabansu, Sheikh Zakzaky fasfo dinsa na fita waje don neman lafiyarsa.

Umar ya ce, mun yi kicibus da ayarin motocin gwamnan jihar a Bakin Ruwa, inda jami’an tsaron da ke a cikin ayarin, suka bude mana wuta a gaban gwaman, inda nan take, mutanen biyar suka mutu wasu kuma suka samu raunuka.

A cewarsa, mun fara jin wasu na yin ikirarin cewa, mun datsewa ayarin motocin gwamnan hanya ne don mu hana shi wucewa, inda ya ce, wannan ikirarin ba gaskiya bane domin ba mu tare masa hanya ba domin kowa ya san a nutse muke gudanar da muzahararmu a ko da yaushe.

Sai dai, kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Muhammad Jalige, ya ce rundunar za ta fitar da sanarwa kan ikirarin da kungiyar ta yi.

Jalige, ya ce tuni aka haramta kungiyar saboda ba ta wani ‘yancin gudanar da zanga-zanga a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here