Bin layin cirar Kash ya yi sanadin mutuwar tsohuwa

0
111

Wata tsohuwa da ta je cire kudi a banki ta yanke jiki ta fadi a kasa a safiyar ranarĀ  Alhamis.

Lamarin ya faru ne bayan mutane sun yi dafifi a wani reshen bankin First Banki da ke Jihar Oyo, tun da sanyin safiya domin bin layi cirar tsabar kudi.

Bayan mutanen sun yi layi suna jiran a bude bankin, da misalin 8:50 na safiya wani jamiā€™in tsaron bankin ya bukaci wasu daga cikinsu su shiga cikin harabar, inda aka tanadar wa kwastomomi kujeru.

Sai dai an yi rashin saā€™a tsohuwar ba ta samu shiga ba har aka rufe kofar, kasancewar sabuwa zuwa ce.

Bayan ta farfadowarta sai ta fashe da kuka, inda ta bayyana cewa tana fama da matsanancin rashin lafiya ne kuma tana bukatar kudi.

An yi katari, jamiā€™an tsaro sun zo sun taiamaka watar, wadda ta kasa tafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here