Gobara ta tashi a wani kauye a jihar Jigawa

0
156

Wata gobarar ta sake tashi a kauyen Barebari da ke a mazabar Sankara a Karamar Hukumar Ringim a Jihar Jigawa.

Gobarar ta kone gidaje da dama, rumbunan adana amfanin gona, dabbobi da kuma lalata dukiya mai yawa.

Shugaban karamar hukumar Ringim, Shehu Sule Udi ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar, inda ya ce, irin wannan gobarar ta tashi a kauyen na Barebarida a shekarar da ta wuce, wacce kusan ta kone kauyen baki daya.

A cewarsa, gobarar ta biyu, ta tashi ne a safiyar ranar Asabar da ta wuce, inda ya ce, karamar hukumar ta bayar da kayan agaji ga wadanda iftila’in ya aukawa.

Ya yi kira ga hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) da kuma hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA) da su taimaka wa wadanda iftila’in ya aukawa.

Kakakin jami’an tsaro na farin kaya (NSCDC) na jihar, CSC Adamu Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, gobarar ta tashi ne a ranar 11 ga watan Maris, 2023 a kauyen Barebari da misalin karfe 12:00 na rana.

Ya dangata tashin gobarar da zubar Bola, inda ya ce, babu ran da ya salwanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here