Kwanturolan NIS na Ribas ya ba da tabbacin kare ‘yan kasashen waje a jihar

0
97

Kwanturolan hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) reshen jihar Ribas, James Sunday, ya tabbatar wa ‘yan kasashen waje mazauna Najeriya da masu zuba hannun jari na kasashen waje da ke jihar, cewa su sha kuruminsu za a kare musu harkokin kasuwancinsu da hannun jarinsu gabanin da bayan zaben Najeriya.

Da ya ke magana da ‘yan kasashen wajen ta kafar sadarwa, Kwanturolan ya jaddada kokarin da hukumar NIS ke yi wajen taimaka wa wadanda ba ‘yan NAjeriya ba, ‘yan kasashen waje da ke zaune a Najeriya, ‘yan kasashen waje da ke nemin izinin aiki, neman izinin zama da yin kaura ta musamman (SIS).

Kazalika da wadanda ba ‘yan NAjeriya ba (Maza) da ke neman auren mace ‘yar NAjeriya bayan cika dukkanin ka’idojin da hakan ke bukata da kuma wadanda suke gudanar da harkokin kasuwancinsu bisa doka da ka’ida tare da cikakken izini ko wasu da ke da wani aikin yi na musamman a cikin kasar nan.

Ya kara da cewa dukkanin wadannan rukunin mutanen (Yan kasan waje) da su kwantar da hankalinsu su ji kamar a gidajensu ko kasashensu na asali su ke domin cigaba da bunkasa harkokin kasuwanci.

A cewar wata sanarwar daga sashin yada labarai na hukumar a jihar Ribas, James ya kuma bukaci ‘yan kasashen wajen da su cigaba da mutunta dokoki da ka’idojin Najeriya da aka shimfida musu tare da bada wa ‘yan Nijeriya suke aiki da su domin rage matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa.

‘Yan kasashen waje mazauna Ribas sun samu tabbacin cewa za a basu cikakken kariya da harkokin kasuwancinsu muddin za su cigaba da mutunta dokoki da ka’idojin dukkanin hukumomin da suka shafi shige da fice da kuma zama halastaccen masu zuba hannun jari a Ribas da ma NAjeriya.

James Sunday ya kuma ba su tabbacin cewa kofar su a bude take wajen kyautatawa da inganta kyakkyawar alaka a tsakanin hukumar ta NIS da ‘yan kasashen waje domin bunkasa hada-hadar kasuwanci da zuba hannun jari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here