AKTH za tai gwajin cutar kansar mahaifa kyauta ga mata

0
185
  • Asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH) Kano na gayyatar mata don duba cutar kansar mahaifa kyauta.

KANO FOCUS  ta ruwaito cewa, sashin kula da cutar sankara na asibitin ne suka gudanar da aikin tantancewar tare da hadin gwiwar Cibiyar Kula da Lafiya da Ci gaban kwararru.

Wata sanarwa da mataimakiyar daraktar hulda da jama’a ta asibitin, Hajiya Hauwa Mohammed Abdullahi ta ce, an shirya fara tantancewar daga gobe Litinin 13 ga Maris 2023 zuwa karshen wata.

Sanarwar ta bayyana cewa, aikin tantancewar kyauta wani bangare ne na ayyukan bukin watan cutar daji ta duniya na shekarar 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here