Barcelona na fuskantar tuhumar bawa alkalan wasa cin hanci

0
205

Barcelona na fuskantar tuhuma kan zargin cin hanci da rashawa da kungiyar ta biya Jose Maria Enriquez Negreira tsohon mataimakin shugaban kwamitin alkalan wasan Spain.

A watan da ya gabata ne Barca ta biya Negreira da wani kamfani da ya mallaka jimlar Yuro miliyan 8.4 tsakanin 2001 da 2018.

Wata kotu a Barcelona ta saurari karar cewa an tuhumi Barca da tsoffin jami’an kulob din da Negreira da laifin cin hanci da rashawa da cin amana da kuma samun su da bayanan kasuwanci na karya.

Wadannan kararrakin da ofishin mai shigar da kara na Barcelona ya gabatar, sun shafi kungiyar ne, da kuma tsoffin shugabanninta wato Josep Maria Bartomeu da Sandro Rosell.

“FC Barcelona ta kulla wata yarjejeniyar magana ta sirri tare da Jose Maria Enriquez Negreira ta yadda, a matsayinsa na mataimakin shugaban kwamitin sulhu yin wani aiki, da nufin aiwatar da ayyukan da zasu taimaka wa Barcelona, a cikin hukuncin da alkalan wasa za su yanke,” in ji ofishin mai gabatar da kara.

A watan da ya gabata ne, shugaban zartarwa na hukumar shirya gasar La Liga, Javier Tebas, ya ce shugaban Barcelona na yanzu Joan Laporta, ya kamata ya yi murabus idan ya kasa bayyana kudaden da aka biya.

Sai dai Laporta, ya mayar da martani da cewa ba zai bai wa Tebas “abin da yake so ba ta hanyar yin murabus” kuma tuhumar ta zo ne kwanaki uku bayan Laporta ya dage cewa kungiyarsa “ba ta taba bawa alkalan wasa cin hanci ba”.

Kocin Barcelona Xavi, wanda ya lashe kofunan La Liga takwas tare da su a matsayin dan wasa tsakanin 1998 zuwa 2015, ya ce bai da masaniya kan kudaden da aka biya kuma bai taba tunanin kungiyarsa na da wata alaka da ta shafi wannan tuhuma ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here