Wata mata ta maka mijinta a kotu kan kwanciyar aure

0
218

Wata ’yar kasuwa ta maka mijinta a kotu saboda zargi rashin ba ta hakkinta na kwanciyar aure.

Matar ta garzaya Kotun Kwastomari da ke yankin Nyanya a Abuja ne a ranar Alhamis, cewa mijinta ya dauki tsawon lokaci ba ya kusantar ta, sannan bai damu da halin da ta shiga ba, ballantana ’ya’yansu.

“Karara ya hana ni hakkina na kwanciyar aure; bai damu da halin da na shiga ba, ya ki gane cewa  aure ba wai kawo wa iyali abinci ba ne kawai.

“Ai duk magidancin kirki ya damu da abin da matarsa take so,” in ji ta.

Don haka ta roki alkalin kotun ya raba aurensu, tana mai zargin mijin nata da rashin sanin ya kamata.

Ta kuma bukaci kotu ta ba ta ikon kula da ’ya’yansu, sannan ta umarci mahaifin nasu ya rika bayar da N100,000 duk wata a matsayin kudin kula da su.

Sai dai kuma wanda ake zargin ya musanta zargin da matar tasa take masa.

Bayan sauraron bangarorin, alkalin kotun, Labaran Gusau, ta dage shari’ar zuwa ranar 30 ga watan Maris.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here