An sace wayar sanata a taron karbar shaidar cin zabe

0
201

Sanata Orji Uzor Kalu ya ce an sace masa wayar hannu a lokacin taron mika takardar shaidar cin zabe ga zababbun ’yan majalisar dokoki ta tarayya.

Orji Kalu wanda shi ne tsohon Gwamnan Jihar Abiya, ya sanar da haka ne tare da jan hankalin mutane cewa su yi hattara da duk wanda zai yi magana da su ta lambobin wayarsa.

Ya ce, “An sace wayata mai dauke da lambobina na MTN da Glo  a lokacin taron mika takardar shaidar cin zabe da ya gudana a Cibiyar Taro ta Ƙasa da Kasa da ke Abuja

“Na sanar da kamfanonin sadarwa amma duk wanda ke da bayanin da zai taimaka, muna bukata,” in ji shi kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Uzor Kalu ya lashe zaben Sanatan Abia ta Arewa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023, karkashin inuwar jam’iyyar APC.

A ranar Talata, 7 ga watan Fabrairu, Hukumar Zabe ta Kasa ta mika wa ’yan majalisar da suka ci zaben takardar shaidar nasara a zaben.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here