An fara fafatawa wajen neman shugabancin majalisun tarayya

0
97

A wani wani yanayi na ba-zata, za a kaddamar da majalisar kasa ta 10 a ranar Talata, 13 ga watan Yunin 2023, kwana biyu bayan wa’adin majalisar ta 9 zai kare a  ranar Lahadi 11 ga watan Yuni.

Idan za a iya tunawa cewa majalisar dokoki ta kasa mai ci an bude ta ne a ranar 11 ga watan Yunin 2019. Tsawon rayuwarta zai kare ne a ranar 11 ga watan Yunin 2023 wato Lahadi, ranar da ba a yin aiki, yayin ranar 12 ga watan Yuni ya kasance ranar hutun dimokuradiyya.

LEADERSHIP ta ruwaito cewa, mambobin majalisa ta 10 da aka zaba wadanda suka hada da sanatoci da ‘yan jamalisan wakilai za su karbi shaidar takararsu a ranakun Talata da Laraba 7 da 8 ga watan Fabrairu, bayan da aka bayyana su a matsayin wadanda suka lashe zaben ‘yan majalisar dokokin Nijeriya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, a ranar Asabar da ta gabata yayin wata ganawa da kwamishinonin zabe gabanin zaben Gwamna da na ‘yan majalisar jiha da za a yi a ranar 11 ga Maris, ya bayyana cewa ta fuskar wakilcin jam’iyya, majalisar kasa ta 10 mai zuwa ita ce mafi yawan bambancin tun 1999.

Ya ce a zuwa yanzu dai a majalisar dattawa, jam’iyyar APC mai mulki ta samu kujeru 57, yayin da babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta samu kujeru 29.

Sauran sun hada da APGA wacce ta samu guda, Jam’iyyar LP ta samu 6, Jam’iyyar NNPP ta samu 2, SDP ta samu 2, sai kuma YPP wacce ta samu daya.

A majalisar wakilai kuwa, APC ta lashe kujeru 162, PDP ta samu 102, APGA ta samu 4, LP ta samu 34, NNPP na da 18, SDP tana da 2, YPP ta samu 1, sannan kuma ADC ta samu 2.

Idan aka yi la’akari da wannan tsari na sama jerin yawan jam’iyyun, zaben shugabannin majalisun biyu na 10 zai yi matukar zama mai abun sha’awa.

Gabanin kaddamar da majalisar dokokin kasar karo na 10 a ranar 13 ga watan Yunin 2023, wasu zababbun ‘yan majalisa sun fara fafutukar neman shugabancin majalisar dattawa da shugaban majalisar wakilai.
Baya ga shugabancin majalisar dattawa da shugaban majalisan wakilai, sauran mukaman da za a nada sun hada da na mataimakin shugaban majalisar dattawa da mataimakin shugaban majalisar wakilai.

Sakamakon binciken LEADERSHIP ya nuna cewa an fara zawarcin ofisoshin a tsakanin jam’iyya mai mulki tare da zababbun ‘yan majalisar dattawa da zababbun ‘yan majalisar wakilai na jam’iyyar APC da ke kokarin ganin ba a sake kuskuren 2015 a zaben shugabannin majalisar ba, inda aka zabi Sanata Bukola Saraki a matsayin shugaban majalisar dattawa, sannan aka zabi Yakubu Dogara a matsayin shugaban majalisar wakilai sabanin zabin jam’iyya mai mulki.

Duk da cewa jam’iyyar APC mai mulki, wadda tabbas za ta samu rinjaye a majalisun biyu na 10, har yanzu ba ta fito da wani tsari na shiyya-shiyya ko raba madafun iko na gwamnati mai zuwa karkashin jagorancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba, tuni wasu daga cikin zababbun ‘yan majalisar tuni suka shiga tattaunawa ta bayan fage domin samun manyan mukaman a majalisar dokokin kasar da za ta fara aiki a ranar 13 ga watan Yuni.

Wadanda suka nuna sha’awarsu na zama shugaban majalisar dattawa ta 10 sun hada da zababben Sanata Orji Uzor Kalu (daga Abia ta Arewa), zababben Sanata Godswill Akpabio (daga Akwa Ibom ta arewa masu yamma), zababben Sanata Ali Ndume (daga Borno ta Kudu), da Sanata Jibrin Barau (daga Kano ta arewa).

Yayin da Kalu, Ndume da Barau suka kasance mambobi a majalisan dattawa ta 9 a halin yanzu, sai dai shi Akpabio ya kasance dan majalisar dattawa ta 8, wanda ke shirin komawa majalisar dattawa na 10.

Sai dai LEADERSHIP ta yi amanna cewa shugaban majalisar dattawa na yanzu, Ahmed Lawan, dan jam’iyyar APC daga yankin Yobe ta Arewa zai so ya ci gaba da rike mukaminsa idan akasarin sanatoci suka mara masa baya. Amma lokaci ne kawai zai nuna.

A halin da ake ciki a majalisar wakilai kuwa, shugaban majalisan na yanzu, Femi Gbajabiamila, wanda ke zama na hannun daman zababben Shugaban kasa, Bola Tinubu, na iya son gwada sa’arsa don ya ci gaba da rike mukaminsa a majalisa mai zuwa. Zai hau kan tasirin Tinubu don yin hakan idan lokaci ya yi.

Kafin hakan ta faru, Gbajabiamila zai samu manyan abokan hamayyar da zai yi takara da su wadanda suka hada da Hon. Ado Doguwa daga Jihar Kano da Hon. Aliyu Betara daga Jihar Borno da kuma sauran jiga-jigan ‘yan majalisa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here