Gwamna Ganduje ya nada sabuwar alkalin alkalai

0
101

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya nada Mai Shari’a Dije Abdu Aboki a matsayin Alkalin Alkalan na Jahar.

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis.

Nadin mai shari’a Aboki ya biyo bayan ritayar da babban alkalin kotun, Mai shari’a Nura Sagir ya yi.

Mai shari’a Aboki ta kasance mai shari’a a babbar kotun jihar tun a shekarar 2006, kuma kafin a nada ta a matsayin babbar alkali, ta taba zama lauyan jiha a shekarar 1985 a karkashin ma’aikatar shari’a ta jihar, inda daga bisani aka nada ta Alkali a shekarar 1986 kuma ta zama mai shari’a. Alkalin babbar kotu a 2006.

Ta kasance memba na kungiyoyi masu sana’a daban-daban kuma ta rike mukamai da yawa. Nadin nata ya fara aiki nan take.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here