‘Yan bindiga sun kashe mutane 6, sun sace mutane 50 a Neja

0
109

Wasu ‘yan bindiga a ranar Talata da daddare sun kashe mutane shida ciki har da wata mata mai juna biyu a kananan hukumomin Rafi da Wushishi na jihar Neja.

Wata majiya daga yankin ta shaida wa LEADERSHIP cewa ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da mutane akalla 50, wadanda suka yi ta’adi a kewayen Anawanka, Sabon Gari da Kundu na kananan hukumomin biyu.

Haka zalika an samu labarin cewa wani jirgin yakin rundunar sojojin saman Nijeriya (NAF) ya yi wa ‘yan bindigar barin wuta na tsawon sa’o’i da dama amma har yanzu ba a san adadin da aka dakile ba.

Kwamishinan tsaron cikin gida da jin kai na jihar Neja, Emmanuel Umar, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce har yanzu gwamnati ba ta tantance cikakken bayanin harin ba.

Jihar Neja na daya daga cikin jihohin Arewa da ‘yan bindiga suka addaba, lamarin ya yi sanadin mutuwar mutane da dama sannan ya raba dubbai da muhallan su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here