Kungiyar ‘yan ta’adda ta IPOB ta Kai wa ‘yan kasuwar Enugu hari

0
104

Rundunar ‘yan sandan Jihar Enugu ta tabbatar da cewa an dakile harkokin kasuwanci a jihar karkashin dokar da IPOB ta aiwatar ta zaman gida dole a duk ranar Litinin.

‘Yan ta’addar karkashin jagorancin Simon Ekpa na kungiyar masu rajin kafa kasar Biyafara (IPOB), sun kai farmaki a wasu sassan jihar, inda suka kone motoci kirar Sienna guda biyu da Keke NAPEP.

Wasu shaidun gani da ido sun shaida wa Leadership Hausa cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Litinin a tashar mota ta Liberty Bus Stop da ke Abakpa a karamar hukumar Enugu ta Gabas.

‘Yan bindigar, a cewar shaidun gani da ido, sun kai farmaki ne a tashar motar bas din da ta kasance mai yawan hada-hada da misalin karfe 05:30 na safe, inda suka yi ta harbe-harbe nan take, don tsoratar da mazauna garin, wadanda ke fitowa daga gidajensu domin gudanar da harkokinsu na kasuwanci.

An ce ‘yan bindigar sun koma babbar hanyar T-Junction, inda suka yi yunkurin tilasta wa wani dattijo daga motar msa kafin su kone shi a cikin motar.

Da yake mayar da martani, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, ya ce zaman lafiya ya daidaita a yankin.

Sai dai ya ce ba a samu asarar rai ba, inda y jaddada cewa ‘yan bindigar tuni suka fice daga yankin.

Ndukwe ya bayyana cewa an samu nasarar kwato motoci biyu da maharan ke amfani da su wajen kai hari, yana mai kira ga jama’a da su taimaka wa rundunar da bayanai masu amfani da za su kai ga kama ‘yan bindigar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here