Sumamen ISWAP ya tilasta wa ‘yan Boko Haram sama da dubu 1 mika wuya ga sojin Najeriya

0
96

Akalla mayakan Boko Haram dubu 1 da dari 2 da 50 tare da iyalansu da ke tserewa ne suka mika wuya ga dakarun Najeriya a arewa maso gabashin kasar a cikin kwanaki 7 da  suka wuce, biyo bayan wani kazamin rikici tsakaninsu da  ISWAP, wanda ya yi sanadin mutuwar ‘yan ta’adda 200.

Mayakan ISWAP sun tarwatsa na Boko Haram, inda suka kashe da dama daga cikinsu, kana suka tilasta wa wadanda ke da sauran shan  ruwa arcewa daga sansanoninsu tare da iyalansu.

Wani kwararre a kan abin da ya  shafi yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi, Zagazola, ya bayyana yadda mayakan ISWAP suka kai harin ramuwar gayya a kan ‘yan Boko Haram a ranakun 26 da 27 ga watan Fabrairun wannan shekarar a garuruwan Gaizuwa, Mantari, Gabchari, Kashimiri, da Maimusari a karamar hukumar Bama ta jihar Borno.

Mayakan na ISWAP sun kuma kai sumame a wata mabuyar mayakan Boko Haram a ranar 1 ga watan Maris, inda suka sake kashe tarin ‘yan Boko Haram.

Majiyoyi daga rundunar sojin Najeriya sun tabbatar da aukuwar wannan lamari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here