Kungiyar ‘yan ta’addan ISWAP ta kashe ’yan Boko Haram 200 a Borno

0
125

Akalla mayakan Boko Haram 200 da matansu da yara kanana ne kungiyar ISWAP ta kashe a wani kazamin fada a Arewa maso Gabashin Gudumbali a Jihar Borno.

Rahotanni sun nuna ’yan ISWAP sun kai hari kan daruruwan ’yan Boko Haram da iyalansu a kauyen Choliye a lokacin da suke tsere wa hare-hare ISWAP..

Wata majiyar soji da ke da masaniya kan lamarin ta shaida wa Zagazola Makama, kwararre kan harkokin tsaro kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, cewa ’yan ta’addan sun tsere daga maboyarsu tsakanin ranar 26 zuwa 27 ga watan Fabrairun 2023, a daidai lokacin da aka kai munanan hare-hare a yankunan Gaizuwa, wanda aka fi sani da Mantari, Gabchari, Kashimiri, da Maimusari a Karamar Hukumar Bama.

Majiyar ta ce hare-haren da ake kaiwa na korar daruruwan mayakan Boko Haram da aka yi wa kawanya, zuwa tsaunin Mandara da ke yankin Gwoza, wasu kuma zuwa Konduga, Mafa da Dikwa, Gajiram, da gabar Tafkin Chadi.

Ta ce wasu kwamandokin Boko Haram sun tsere amma ISWAP ta kara tura wasu mayaka suka bi su, suka kama su a kauyen Choliye, inda suka bude musu wuta suka kashe ‘yan ta’adda 200 da iyalansu, yawancinsu mata da kananan yara.

Majiyar ta ce ISWAP ya kashe mayaka da kwamandojin Boko Haram da dama a ranar 1 ga Maris,  a yankunan Asinari, Ashanari, da Masarmari a Konduga.

“A kauyen Yale da ke Karamar Hukumar Konduga, ISWAP ta kai mummunan hari a kan ’yan Boko Haram, wanda ya tilasta wa daruruwan mayakan Boko Haram da iyalansu mika wuya ga sojojin Operation Hadin Kai da ke Mafa, Konduga, da sauran sassan rundunar OPHK  yayin da wasunsu suka tsere ta hanyar Mafa zuwa Dikwa, Abadam, kamar yadda ya ce.  da Jamhuriyar Nijar a yankin tafkin Chadi.”

Rikicin da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin Boko Haram da ISWAP da alama ba zai kare ba yayin da kokarin da kungiyoyin ke yi na hada karfi don yakar sojojin Najeriya da rundunar hadin gwiwa ta Multinational Joint Task Force (MNJTF) ba zai yiwu ba.

ISWAP da Boko Haram dai, ya zuwa yanzu, sun mayakansu a yayin da suke ci gaba da kai wa juna hari, inda suka yi barna a tsakaninsu.

A ranar 6 ga Disamba, 2022, Boko Haram ta kai daya daga cikin munanan hare-hare, inda suka kashe mata 33 na mayakan kungiyar ISWAP a Dajin Sambisa.

A ranar 31 ga watan Disamba, wani bangare na kungiyar Boko Haram ya kai hari a sansanin ISWAP da ke Toumbum Allura Kurnawa da Kangar da ke gabar tafkin Chadi.

A bisa haka ne ISWAP ta tsere daga Najeriya zuwa Somalia, Mali, da Burkina Faso don neman goyon bayan sauran abokan ta’addancinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here