‘Yan bindiga sun kashe DPO da wani dan sanda a Zamfara

0
98

Wasu ‘Yan bindiga sun kai hari a ofishin rundunar ‘yan sanda reshen Maru a jihar Zamfara, inda suka kashe babban jami’in ‘yan sanda na yankin (DPO) da wani Sajan.

An kai harin ne da yammacin ranar Asabar a lokacin da ‘yan bindigar suka yi yunkurin yin garkuwa da wani dan kasuwa mai suna, Alhaji Iliya, wanda gidansa ke daura da hedikwatar ‘yan sanda da ke karamar hukumar Maru a jihar.

LEADERSHIP ta rawaito cewa, ‘yan bindigar sun bude wuta kan jami’an ‘yan sandan da ke ofishin, inda suka kashe DPO da wani dan sanda mai mukamin Sajan.

Kazalika ‘yan bindigar sun kuma yi garkuwa da wata mata.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan jahar Zamfara, SP Mohammed Shehu, ya ki cewa komai game da harin, inda ya ce sun je Maru ne domin duba halin da ake ciki amma za su tuntubi wakilin mu idan ya koma Gusau, babban birnin jahar Zamfara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here