‘Yan bindiga sun harbe wani dagaci a Kano

0
95

An harbe dagacin kauyen Maigari da ke karamar hukumar Rimin Gado a Kano, Dahiru Abba.

Dan sa wanda shi ne Shugaban Karamar Hukumar Rimin Gado, Barista Munir Dahiru Maigari, ya tabbatar wa Jaridar Daily Trust faruwar lamarin.

Maigari ya ce, “Abin ya faru ne da misalin karfe biyu na dare inda suka zo suka yi abin da suka yi.

“Ba za mu iya cewa komai ba dangane da musabbabin abin da ya faru a yanzu, amma ya rasu kuma muna addu’ar Allah ya jikansa da rahama.”

Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun kutsa cikin gidan dagacin inda suka far masa suka bude masa wuta.

Ya bayyana cewa za a yi jana’izarsa a gidansa da ke kauyen Maigari a yau Lahadi.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce bai san da faruwar lamarin ba amma zai yi bincike kan lamarin.

Kano dai na daga cikin Jihohin da suke cikin kwanciyar hankali a tabarbarewar tsaro a yankin Arewa maso Yamma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here