Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Ayu, Okowa, za su jagoranci zanga-zanga a hedkwatar INEC ta kasa

0
101

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu da dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Gwamna Ifeanyi Okowa za su jagoranci wasu jiga-jigan jam’iyyar a wata zanga-zanga da suka shirya zuwa  hedikwatar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ke Abuja ranar Litinin.

INEC ta bayyana Bola Tinubu, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a matsayin wanda ya lashe zaben kuma zababben shugaban kasa na zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Tinubu ya samu kuri’u 8,794,726 inda ya doke Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP mai kuri’u 6,984,520, sai Peter Obi na jam’iyyar Labour Party (LP) wanda ya samu kuri’u 6,101,533.

Amma Atiku da PDP sun yi watsi da ayyana Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa, inda suka ce zaben na cike da kura-kurai kuma za su kalubalance shi a kotu.

Jam’iyyar adawa a wani mataki da ake ganin yana daya daga cikin hanyoyin kalubalantar sakamakon ta sanar da mambobinta cewa za a gudanar da zanga-zanga a gobe da safe a harabar ofishin INEC. 

A sanarwar da Daraktan Gudanarwa na Majalisar Kamfen din Shugaban kasa na PDP, Ibrahim Bashir, jam’iyyar ta fitar ta sanar da mambobinta cewa za a fara zanga-zangar ne daga gidan Legacy da ke unguwar Maitama da karfe 10 na safe.

“An umurce ni da in gayyace ku cikin girmamawa: Shugaban jam’iyya, Dokta Iyrochia Ayu, mataimakin dan takarar shugaban kasa kuma gwamnan jihar Delta, Dr. Ifeanyichukwu Okowa. 

“Gwamnonin; Akwa Ibom da Shugaban kamfen din dan takarar shugaban kasa , Mr Udom Emmanuel, gwamnan Sokoto kuma DG na kamfen din dan takarar sugaban kasa na PDP, Rt Hon Aminu Waziri Tambuwal, da gwamnonin Bayelsa, Edo, Adamawa, Bauchi, Taraba da Osun. 

“Tsoffin shugabannin majalisar dattawa, Sanata David Mark da Sanata Dr Abubakar Bukola Saraki, mambobin kwamitin amintattu na PDP, Sanatocin PDP da ‘yan majalisar wakilai, mambobin jam’iyyar, daraktoci, mataimaka da mataimakan daraktoci da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here