Jami’ar ABU za ta ƙirƙiro mota mai amfani da ruwa a madadin fetur

0
109

Shugaban tsangayar ilimin fasaha a Jami’ar Ahmadu Bello, ABU, da ke, Zariya, Farfesa Ibrahim Dabo, ya ce jami’ar na shirye-shiryen kera wata mota, kirar gida Najeriya da za ta rika amfani da ruwa a maimakon fetur.

Shugaban ya bayyana haka ne a jiya Asabar a Zariya, yayin da ya ke zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙas a kan bikin ranar Injiniyanci ta Duniya na 2023 don samun ci gaba mai dorewa.

Farfesa Dabo, ya ce an samu ci gaba da dama a ABU, ciki har da samar da wata motar tsere.

A nan ne ya kara da cewa jami’ar tana aikin samar da wata mota da za ta rika tafiya da ruwa maimakon man fetur.

“Motar tseren da jami’ar ta kera tana da karfin tafiyar kilomita 100 a kan litar mai ɗaya tak,” in ji shi.

A cewarsa, an kai wannan motar zuwa Afirka ta Kudu inda kuma tana nan ta na aiki yadda ya kamata.

Ya jaddada cewa jami’ar na kokarin inganta shan man motar.

“Ma’anar motar wata karamar mota ce da ke daukar mafi yawan mutane biyu don gasar tsere, ba don zirga-zirgar jama’a ba,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here