Matsayar doka kan takaddamar sakamakon zaben bana – Masana

0
97

Masu ruwa da tsaki a bangarori daban-daban na ci gaba da bayyana ra’ayinsu a kan daukar matakin da Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta yi na ci gaba da karbar alkaluman sakamakon zaben shugaban kasa, duk da bukatar dakatar da hakan daga bangaren ’yan adawa.

Tuni dai INEC ta bayyana dan takarar Jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara a zaben.

Takaddamar ta fara ne a yammacin ranar Litinin a zauren tattara sakamakon zaben shugaban kasa da ya gudana, inda wakilin babbar jam’iyyar adawa ta PDP a wajen, Sanata Dino Melaye ya yi korafi cikin zafafan kalamai kan rashin dora sakamakon a shafin hukumar na intanet, kamar yadda tun farko hukumar ta yi alkawarin yi.

Wakilin na Jam’iyyar PDP ya samu goyon bayan karin wasu jam’iyyu 5 ciki har da ta LP, inda suka fice daga zauren a matsayin bore.

Sai dai wasu jam’iyyu 11 da suka hada da NNPP, sun ci gaba da kasancewa a cikin zauren taron, inda suka bukaci INEC da ta ci gaba da karbar bayanin sakamkon zaben daga jihohi.

Bayan wasu ’yan sa’o’i kadan sai kuma tsohon Shugaban Kasa Olusegubn Obasanjo, shi ma ya shiga lamarin bayan ya bayyana a kafofin yada labarai yana goyon bayan masu bukatar dakatar da sakamakon zaben.

Cif Obasanjo ya kuma bukaci hukumar da ta rusa zabuka a yankunan da aka samu takaddama tare da tsara mata ranar Asabar a matsayin lokacin da za ta sake zabuka a yankunan.

Sai dai jawabin na Obasanjo ya gamu da cikas, inda wasu kungiyoyin sa ido na kasa da kasa da suka hada da Kungiyar Kasasehe Renon Ingila (Commonwealth) da ta kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) suka bayyana goyon bayansu ga zaben.

Haka ita kanta jam’iyyar da ta samu nasara (APC) ta yi misalai da sakamokn zabukan da suka gudana a Jihar Legas, inda dan takararta ya fito da kuma na Jihar Katsina ta Shugaban Kasa Buhari, a matsayin wuraren da ta rasa, inda ta ce ’yan adawar ba su yi la’akari da su ba.

Aminiya ta ji ta bakin wasu masana shari’a a kan lamarin da suka hada da Barista Mainasara Kogo Umar da kuma Barista Bukar Bulama Bukarti, inda suka yi tsokaci a kai.

Rashin nazarin dokar zabe ne

A nasa bangaren, Barista Mainasara Kogo ya ce da bangarorin biyu za su yi amfani da abin da doka ta ce, da tun farko ba a fuskanci takaddamar ba.

Ya ce ya kamata tun a farko bangarori biyun da ke takaddamar su yi nazari kan abin da dokar da ta kafa hukumar zabe ta INEC ta ce a sashi na 153 kan na’urar tantace zabe da kuma aikawa da sakamakonsa ta intanet, wanda ya ce ke matsayin wata dama da aka ba ta.

Baristan ya ce akwai kuma sashi na 65 da ya bai wa hukumar damar samar da maslaha idan aka samu wani kure da kuma hanyar da ya kamata a bi idan akwai korafi ko rashin gamsuwa.

Lauyan ya ce sashi na 76 na dokar zaben ya ba da damar garzayawa zuwa kotu don warware takaddama da ka iya bijirowa a kan lamarin.

Ya kuma lisafto wasu sassa a dokar da ta kafa hukumar ta zabe, inda ya ce dokar kasa ta bai wa duk wani mai korafi damar gabatar da bukatarsa a cikin tsanaki da nuna biyayya ga hukumomi da dokar kasa, sabanin yadda shi mai korafin ya gabatar da kansa.

Ya bayyana mamakinsa a kan rashin shawo kan matsalar tun daga matakin rumfunan zabe, inda ake bukatar duk wani wakilin jam’iyya ya sa hannu gabanin tattara sakamakon zuwa mataki na gaba.

“Tun daga matakin rumfunan zabe ya kamata wakilin jam’iyya zai nuna rashin amincewarsa ta hanyar kin sa hannu, har sai an sanya sakamakon a intanet,” inji masanin.

A tilasta wa jami’an INEC sanya sakamako a intanet

Barista Kogo ya kuma bukaci INEC da ta karfafa ka’idar doka ta hanyan tilasta wa duk wani babban jami’in tattara sakamakon zabe na tabbatar da cewa an samu sanya hannu na kowane wakilin jam’iyya a takardar sakamako, gabanin ba shi damar gabatar da bahasinsa.

Sai dai ya ce sabanin hakan, jami’an INEC na barin takardun tun a mataki na jiha, ba tare da la’akari da cewa bukata ka iya tasowa da zai sa a tilasta neman takardun.

Masanin ya ce yawancin ’yan siyasa sun yanke kauna kan shari’o’i da ke gudana a kotuna bayan gabatar da sakamakon zabe, da ya ce hakan ke sa suke neman sama wa kansu hakki tun daga matakin hukumar zabe.

Ya bukaci jam’iyyu da mambobinsu da kuma hukumar zabe da su rika bin ka’idar aiki kamar yadda doka ta tsara.

Sannan ya bukaci da a kafa dokar hukunta duk wani jami’in zabe da aka samu da hannu wajen kin aiki da na’urar zabe ko hana ta yin aiki.

Ya ce rashin bin doka da oda ko hukunta mai laifi ya yi kamari a karkashin gwamnati mai barin gado, inda ya ce ko shi kansa jami’in jam’iyyar da ya yi korafi, mai karya doka ne; inda ya yi misali da dirkowa da ya yi daga cikin mota a yayin da aka kama shi a wani lokaci, don fuskantar wata shari’a, wanda ya ce ya saba doka.

INEC ta yi daidai

Ya ce Hukumar INEC ta yi daidai wajen yin gaba-gadi kan ayyana sakamakon zaben, duk da bukatar ta ’yan adawa na jingine shi.

Ya ce jan kafa tare da yin jinkiri kan sanar da sakamakon na iya kara ta’azzara matsalar tare da shiga hakkin wasu da suke ganin su ke da rinjaye, a maimakon bin hanyar da doka ta tsara ta neman bahasi a kotu kan abin da ba a gamsu da shi ba.

Ya ce korafin da ’yan adawar suka gabatar, ikirari ne na baki da ya kamata a gabatar da shi a rubuce tare da mikawa tun a farko, a maimakon jinkirta yin hakan har sai bayan gabatar da shi a zauren tattara sakamako.

Barista Mainasara ya kuma yi Allah wadai da jinkiri da aka samu na sakar wa Hukumar ta INEC ruwan kudi da take bukata har zuwa ranar Laraba, ana kwana uku da ga zabe, wanda ya ce lallai hakan ka iya taka rawa wajen gudanar da wasu ayyukanta na kar-ta-kwana kamar na biyan kudin alawus ga jami’anta na wucin gadi da suka hada da jami’an tsaro da masu jigilar kayan aiki da dai sauransu.

Ya ce jinkirin da aka samu bai rasa nasabar haddasa fara aiwatar da zaben na ranar Asabar a makare a wurare, kamar yadda ya ce a ka gano daga bisani.

Bai kai a rusa zaben ba

Haka shi ma wani masanin shari’a kuma mai fafutikar kare hakkin jama’a mai suna Barista Bukar Bulama Bukarti, ya ce kodayake ba za a iya cewa masu korafin ba su da tushe ko makama a doka ba, sai dai a bukatar tasu ba ta kai na a rusa zaben dungurugum ba, kamar yadda Jam’iyyar PDP ta nemi a yi ba.

Ya ce kundin zabe da suka kafa hujja da shi, wanda ya nemi a tura sakamakon zabe ta intanet bayan aiwatar da shi, kama daga mazaba ta unguwa zuwa ta gunduma da ta karamar hukuma da jiha, har kuma zuwa Abuja, bai fayyace amfani da wata ayyanannar na’ura ba.

Ya ce dokar ta bai wa hukumar damar yin abin da ya dace kan radin kanta da ake kira “Guide line” inda ya ce kuma da wannan ne Hukumar ta INEC ta sanar da cewa za ta yi hakan ne da na’urar tantacewa da aikawa da sako ta BVAS.

“Sai ga shi an samu akasi ta gaza yin hakan a wasu wurare.

“Sai dai duk da hakan babu inda doka ta ce rashin aiwatar da hakan na kaiwa ga daukar matakin jingine sanarwar ko soke na wani bangare ko zaben dungurugum ba,” in ji Bulama Bukarti.

Ya ce dokar cewa ta yi za a iya soke zaben ne idan aka fuskanci mummunan rashin bin ka’ida da ya kai ga sauya tsarin sakamako, wanda kuma a cewarsa babu irin hakan a wannan lamari saboda rashin dora sakamakon a kan intanet bai haifar da sabanin a mummunan mataki ba, idan har ma akwai.

INEC da Buhari ba su da hurumin soke zabe

Bukarti ya ce shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmud Yakubu da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba su da hurumin soke zabe kamar yadda tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya bukaci su yi.

“Idan aka ce za a soke da kuma sake yin zaben, to za a kashe wani kudi Naira biliyan 40 ke nan, sannan kuma bayan an sake yin wani zaben wasu za su sake bukatar da a rushe shi kamar yadda yake faruwa a duk wani zabe komai sahihancinsa.

“Abin da ya dace a yi shi ne, masu korafi su gabatar da kukansu ga kotu, wadda ita ce ke da hurumin tantacewa da kuma yin hukunci a kai,” inji shi.

Aminiya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here