‘Yan sanda sun kama zababben dan majalisar NNPP kan daukar bindiga a yakin neman zabe

0
116

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano tana ci gaba da tsare zababben dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Dala ta a Jam’iyyar NNPP, Aliyu Madaki.

Tun a ranar Larabar ne Ali Madaki ya amsa gayyatar da ’yan sanda suka yi masa bayan bidiyonsa yana dauke da bindiga a wani gangamin siyasar dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar NNPP, Rabi’u Kwankwaso, ya bayyana a intanet.

A tattaunawar da Aminiya ta yi da Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta wayar tarho a safiyar Alhamis ya bayyana cewa har yanzu Ali Madaki yana hannunsu ana ci gaba yi masa tambayoyi.

Aminiya ta rawaito cewa wasu ’yan daba sun kai hari kan ayarin motocin ’yan jam’iyyar NNPP a kan titin Zariya-Kano a ranar 23 ga watan Fabrairu, a babban taron yakin neman zaben shugaban kasa Kwankwaso, kuma ana zargin Ali Madaki ya jagoranci murkushe ’yan dabar.

Lamarin ya kai ga jami’an tsaron suka cafke shugaban Karamar Hukumar Ungogo Abdullahi Ramat da Shugaban Karamar Hukumar Riminga, Munir Dahiru dauke da bindigogi.

Daga bisani ’yan sanda sun kama wasu ’yan daba 85 tare da shugabannin a yayin rikicin amma sun saki shugabannin kananan hukumomin ba tare da gurfanar da su gaban kuliya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here