Karfe 3 na rana INEC za ta ba wa Tinubu satifiket din cin zabe

0
106

Najeriya ta wayi garin ranar Laraba da Bola Ahmed Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa, bayan ya yi nasara da kuri’u miliyan 8.8 a zaben da aka kammala a ranar Asabar.

Bayan sanar da sakamakon zaben, Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce da misalin karfe uku da yamma za ta mika wa Tinubu takardar shaidar cin zaben shugaban kasa.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce, “Yau da karfe uku na rana hukumar za ta ba wanda ci zabe takardar shaidar samun nasara.

“Wadanda suka yi nasara a zaben ’yan Majalisar Wakilai da Sanatoci kuma, daga baya hukumar za ta sanar da lokacin ba su takardar shaidarsu.”

A ranar Asabar ne ’yan Najeriya miliyan 25.3 suka fita rumfunan zabe da ke fadin kasar, domin zaben shugaban da zai jagoranci kasar na tsawon shakera hudu, bayan karewar wa’adin shugaba mai ci, Muhammadu Buhari, wanda zai sauka dag mulki a ranar 29 ga watan mayu.

A ranar ce kuma ’yan kasar suka kada kuri’ar zaben sanatoci 109 da kuma ’yan Majalisar Wakilai 360 da ake da su a kasar.

Jam’iyyu 18 ne dai suka fafata a zaben na bana, inda manyan jam’iyyun da suka fi tabukawa su ne APC mai mulkin kasar, babbar adawa PDP, sai jam’iyyar LP da kuma NNPP.

Zaben shi ne karo na bakwai daga lokacin da Nejeriya ta sake dawowa kan tafarkin dimokuradiyya a shekarar 1999.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here