DA DUMI-DUMI: Osinbajo ya halarci taron bawa zababban shugaban kasa takardar shedar lashe zabe

0
131

A yammacin Larabar da ta gabata ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta mikawa zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, takardar shaidar lashe zaben shugaban kasa na 2023 da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.

Shugaban INEC kuma babban jami’in tattara sakamakon zabe na tarayya Farfesa Mahmood Yakubu ne ya gabatar da takardar shaidar a cibiyar tattara bayanai ta kasa (NCC) da ke Abuja.

Haka kuma, an baiwa zababben mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima takardar shaidar cin zabe.

Tinubu da Shettima sun kasance tare da matansu a takaitaccen taron da aka fara da misalin karfe 3:30 na rana.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Janar Babagana Monguno (rtd) sun halarci bikin, da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC.

Da yake jawabi bayan an ba shi takardar shaidar lashe zaben, zababben shugaban kasa, Tinubu ya ce takardar shaidar ta nuna cewa kowa zai iya cimma wani buri a rayuwarsa in har yayi yakini da imani.

Ya yi alkawarin yin aiki ba dare ba rana tare da iyakar iyawarsa don ganin Najeriya ta gyaru.

Tun da sanyin safiyar ranar ne Farfesa Yakubu ya ayyana Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin zababben shugaban kasa, saboda ya samu mafi rinjayen kuri’un da aka kada kuma ya cika sharuddan doka.

Tinubu ya samu kuri’u 8,805,655 inda ya doke babban abokin hamayyarsa kuma dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, wanda ya samu kuri’u 6,984,520.

Atiku ya biyo bayan dan takarar jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi wanda ya samu kuri’u 6,098,798 da kuma Rabi’u Musa Kwankwaso na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) wanda ya samu kuri’u 1,496,687.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here