Tinubu ya gana da Jonathan da wakilan ECOWAS a Abuja

0
99

Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da wakilan Kuungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), masu sanya ido kan zabe a gidansa da ke Abuja a ranar Talata.

Tsohon shugaban Ghana, John Mahama, yana cikin tawagar ECOWAS da ta ziyarci Tinubu.

Mahama da Jonathan sun sha kaye a lokaci guda lokacin sa suka nema tazarce.

Tinubu, wanda ke kan gaba a sakamakon zaben shugaban kasa, ya tarbe su sai dai ba a bayyana dalilin ganawar tasu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here