PDP ta lashe kujerar sanatan Kaduna ta tsakiya

0
106

Dan takarar Sanata a Jam’iyyar PDP, Lawal Adamu Usman, wanda aka fi sani da Mista LA, ya lashe kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya.

Sakamakon zaben da Baturen Zabe, Farfesa Haruna Aminu, ya sanyawa hannu ya nuna Mista LA ya samu kuri’u 225,066, shi kuma dan takarar jam’iyyar APC mai mulkin jihar, Abdullahi Muhammad Sani ya samu kuri’u 182,035.

Dan takarar NNPP Umar Ahmad Tijjani ya samu kuri’u 24,395 sannan dan takarar LP, Ibrahim Muhammad Sani ya samu kuri’u 8,7510.

A yanzu dai jam’iyar PDP ce ta lashe dukkan kujerun sanatoci uku da ke a Jihar Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here