Jam’iyyun adawa sun bukaci shugaban INEC ya sauka daga mukaminsa

0
109

Wasu jam’iyyun adawa sun bukaci Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ya sauka daga mukaminsa.

Jam’iyyun PDP, LP da ADP sun yi kiran ne a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Talata.

Julius Abure, shugaban jam’iyyar LP, wanda ya yi magana a madadinsu, ya ce ‘yan Najeriya ba su da kwarin gwiwar gudanar da zaben ne saboda kin yin amfani da na’urar tura sakamakon zabe kamar yadda dokar zabe ta bayyana.

Jam’iyyun sun yi zargi an tafka magudi, tashe-tashen hankali a yayin zaben da aka gudanar a ranar Asabar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here