Tinubu ya samu nasara a jihar Kwara

0
115

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata a dukkan kananan hukumomi 16 na jihar Kwara.

 

Dan takarar jam’iyyar APC ya samu kuri’u 263,572 yayin da dan takarar jam’iyyar PDP, Alh Atiku Abubakar ke mara masa baya da kuri’u 136,909.

 

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Mista Peter Obi, ya samu kuri’u 31,166 ya zo na uku yayin da dan takarar jam’iyyar NNPP, Engr. Rabiu Kwakwanso, ya samu kuri’u 3,141.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here