An kama wasu mutane 15 bisa yunkurin yin kutse a sakamakon zabe a jihar Katsina

0
125

Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina na gudanar da bincike kan wasu mutane 15 da ake zargi da laifin yin kutse a harakokin zaben shugaban kasa da na ‘yan Majalisa.

Yayin da ‘yan Najeriya ke zaben sabon shugaban kasa da wakilansu a majalisar dokokin kasar,Kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, SP Gambo Isa, wanda ya yi wa manema labarai karin haske a yammacin jiya Juma’a, ya ce an kama wadanda ake zargin da na’urorin lantarki da dama da suka hada da na’urori masu kwakwalwa.

‘Yan sanda suna gudanar da bincike kuma za a bayyana sakamakon ga jama’a a cewar SP Gambo Isa.

Jami’in ya bayyana cewa sun gayyaci masana da nufin tantance ainihin manufar wadanan mutane da ‘yan Sanda suka kama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here