An kai wa ma’aikatan zabe hari a Gombe

0
119

Wasu da ake kyautata zaton ’yan bangar siyasa ne sun kai wa ma’aikatan zabe hari a wata mazaba da ke unguwar Tudun Wada a garin Gombe.

Rahotanni sun nuna an kai harin ne a daren ranar juma’a, inda suka yi yi awon gaba da wayoyi tare da raunata wasu daga cikin ma’aikatan gabanin zaben shugaban kasa na ranar asabar.

Shaidun gani da ido sun ce an garzaya da mutum uku asibiti domin kula da su sakamakon raunin da suka samu.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar Gombe, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce ma’aikatan sun je mazabar su kadai ne ba tare da jami’an tsaro da za su yi musu rakiya ba.

A cewarsa, ana zargin ’yan banga ne suka kai harin.

Sai dai ASP Mahid ya ce mace daya ce ta samu rauni daga cikin ma’aikatan zaben, kuma tuni aka garzaya da ita asibiti.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here