An fara kada kuri’a a zaben shugaban kasa

0
107

A yau ne ‘yan Najeriya fiye da miliyan 93 ke kada kuri’a don zaben sabon shugaban kasa da ‘yan majalisar tarayya 468, makwanni 2 gabanin da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha da zai gudana a ranar 11 ga watan Maris.

Babban zaben kasar na bana shi ne zai zama karo na bakwai tun bayan dawo da mulkin dimokradiyya a kasar, bayan zabukan da suka gabata a shekarun 1999 da 2003 da 2007 da kuma 2011 baya ga 2015 da 2019.

‘Yan takara 18 ke fafatawa don kujerar shugabancin Najeriya da nufin maye gurbin shugaba Muhammadu Buhari da ke kammala wa’adi na biyu a mulkin kasar.

‘Yan takarar da ke fafatawar a zaben na yau sun kunshi Christopher Imumolen na jam’iyyar Accord sai Hamza Al-Mustapha na jam’iyyar AA kana Omoyele Sowore na AAC tukuna Dumebi Kachikwu na ADC akwai kuma Yabagi Sani na ADP tukuna Bola Tinubu na APC kana Peter Umeadi na APGA da kuma Gimbiya Ojei daga APM sannan Charles Nnadi na jam’iyyar APP.

Ma'aikantan Ihukumar zaben Najeriya  INEC a Ibadan

Sauran ‘yan takarar sun hada da Sunday Adenuga na BP da Peter Obi na LP kana Rabi’u Musa Kwankwaso daga NNPP sannan Felix Osakwe na NRM da kuma Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP sannan Kola Abiola daga PRP da kuma Adebayo Adewole na SDP sannan Ado Ibrahim Abdulmalik daga YPP sai Dan Nwanyanwu daga jam’iyyar ZLP.

Sai dai duk da yawan ‘yan takarar da ke fafatawa a zaben na Najeriya hudu daga ciki aka fi yiwa hasashen nasara lura da yadda Atiku Abubakar da Bola Tinubu ke da rinjayen magoya baya yayinda a bangare guda Rabi’u Musa Kwankwaso na NNPP ke rike da galibin kuri’un jihohin arewa maso yamma a bangare guda Peter Obi ke da kuri’un Igbo.

Ma su zabe a jihar KanoMa su zabe a jihar Kano

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here