Kotun koli ta tsayar da ranar 3 ga Maris don yanke hukunci kan karar manufofin canjin kudi

0
88

A ranar Laraba ne kotun koli ta kammala sauraren karar da aka shigar gabanta kan gwamnatin tarayya kan manufar sake tsara kudin Naira mai cike da cece-kuce tare da sanya ranar 3 ga watan Maris domin yanke hukunci.

Mai shari’a John Inyang Okoro ya tsayar da ranar ne bayan da ya gabatar da hujja akan karar da wasu jihohin kasar suka shigar.

Jihohin da Kaduna da Kogi da kuma Zamfara ke jagoranta suna neman kotun kolin da ta tarwatsa tare da ajiye manufofin CBN na cewa tana wahalar da ‘yan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba.

Jihohin sun zargi Buhari da yin sama da fadi da ayyukan babban bankin Najeriya CBN, inda suka bukaci a karya dokar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar.

Babban Lauyan shari’a, Abdulhakeem Mustapha ya gabatar da shari’ar jihohin.

Cikakkun bayanai suna zuwa...

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here