Gobara ta lalata kayan biliyan 23 cikin wata 3 a Najeriya — Hukumar kashe gobara

0
134

Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya ta ce gobara ta lalata kayayyakin da darajarsu ta kai Naira biliyan 23 cikin wata ukun karshen shekarar 2022, yayin da mutum 28 suka rasa rayukansu a gobara 649.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin bayananta na kididdiga da ta ba wa Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a ranar Talata a Abuja.

Alkaluman sun nuna an ceto jimillar mutum 29 da dukiyar kimanin biliyan N145.4.

Rahoon ya nuna sabubban gobarar sun hada da matsalar wutar lantarki da kuma fashewar tukunyar gas din girki.

Sauran sun hada da ajiyar man fetur a yanayin da bai da dace ba, gobarar daji, tartsatsin wutar lantarki da dai sauransu.

Ya ce wuraren da abin ya shafa sun hada da gidaje, makarantu, shaguna, otal-otal, gidajen cin abinci, masana’antu, bankuna, gidajen mai, tiransifoma, rumfunan sayar da katako, motoci, kasuwanni, hatsarin jirgin sama da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here