‘Yan sanda sun cafke wasu mutane kan zargin mallakar kudaden jabu a Kebbi

0
110

Rundunar ‘Yansandan jihar Kebbi ta cafke wasu mutum uku da ake zargin su da yin jabun kudi da ya sama da naira miliyan goma sha bakwai (N17,000,000) a garin Warra da ke karamar hukumar Ngaski.

An gano kudaden jabun tare da taimakon kungiyar ma’aikatan sufuri ta kasa (NURTW) a tashar mota ta Warra.

Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Ahmed Magaji Kontagora, ya ce wadanda ake zargin ‘yan asalin kauyukan Gungun Tawaye ne da Chupamini, a karamar hukumar Ngaski, yayin da ake ci gaba da bincike, nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya.

Kwamishinan ya kuma jaddada cewa, wadanda ake zargin sun hada da Faruku Zubairu Musa da Salisu Mohammed dukkansu maza daga Karamar hukumar Ngaski ta jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here