Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 7 a Kaduna

0
124

Sojoji sun yi nasarar kashe wasu ‘yan bindiga bakwai a wani samame da suka kai a yankin Kasso da ke Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna.

An bayyana cewa sojojin sun yi artabu da ‘yan ta’addar a kusa da kauyen Unguwar Rimi da ke garin Kasso.

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na jihar, Mista Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Juma’a.

Ya ce sojojin sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’addan ne bayan barin wuta da suka yi da su.

“An tabbatar da kashe ‘yan bindiga bakwai yayin samamen,” in ji shi.

Ya bayyana cewa sojojin sun kwato babura biyar, harsasai 153 da wayoyin hannu guda uku.

Ya ce gwamna Nasir El-Rufai ya yaba wa sojojin bisa yadda suka nuna kwarewa.

Aruwan ya kara da cewa, gwamnan ya kuma yaba wa Manjo-Janar T.A Lagbaja, ME Ejumabone, Kwamandan sojojin ruwa bisa nasarar gudanar da aikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here