Dan sanda ya harbe wata tsohuwa har lahira a Adamawa

0
232

Wani dan sanda da ke bakin aiki ya hallaka wata tsohuwa mai shekara 65 har lahira a yayin wata takaddama a garin Yola, babban birnin Jihar Adamawa.

Wani ganau, ya bayyana cewa tsohuwar ta gamu da ajalinta ne bayan jama’ar gari sun bukaci bayani kan dalilin da ya sanya ’yan sanda suka kama wani matashi a kofar gidansa a yankin Doubeli a Yola.

Ana tsaka da haka ne rikici ya barke tsakaninsu, inda dan sandan ya bude wuta, lamarin da ya yi sanadin raunata mutum biyu.

Rahotanni sun bayyana cewa harsashi ya samu tsohuwar mai suna Yerbure, wanda ya yi sanadin mutuwarta, lamarin da ya haifar da yamutsi a yankin.

Tuni aka kai gawar matar Asibitin Kwararru na Yola, shi kuma wanda ya ji rauni aka kwantar da shi don yi masa magani.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan ’yan sandan jihar, Afolabi Babatola, ya fitar a ranar Juma’a, ya jajanta wa iyalan marigayiyar.

Ya ce rundunar ta tsare dan sandan da ya yi harbin mai suna Sajan Aliyu Yusuf.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here