Yadda kogin jami’ar ABU ya ci dalibai ’yan gida daya

0
196

Wasu daliban makarantar sakandaren Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ce sun gamu da ajalinsu a kogin cikin jami’ar.

Daliban ’ya’yan mutum daya ne, masu shekaru 13 da kuma 14, inda karamin mai suna Abdulrahman Gaminana ke aji uku a karamar sakandare, wansa Sa’ad kuma ke aji daya a babbar sakandare.

Mahaifiyar yaran, Malama Rashida Musa ta shaida wa Aminiya cewa, “A ranar Talata sun taso makaranta, a kan hanyarsu na komowa gida wajen tsallaka kogi sai igiyar ruwa ta harde su, da yake da karar kwana sai Allah Ya karbi rayuwarsu.”

Malama Rashida ta kara da cewa, dama idan sun taso makaranta mahaifinsu ke dauko su, amma a ranar saboda karar kwana, Allah Bai ba shi iko ba, sai suka tako da kafa, suka biyo ta Anguwar Koraye da ke bayan jami’ar.

Ta ce akwai kogi da ke kai ruwa madatsar ruwar jami’ar, da ake  ratsawa a wuce; to bayan sun shiga sai igiyar ruwa ya ja su suka nitse kamar yadda wani yaro da yake wanki a bakin kogin kuma wanda shi ne ya kira mutane dan a ceto su ya bayyana.

Ta ce da yake suna sanye da kayan makaranta, “sai nan da nan aka sanar da makarantar, inda malamansu suka je wurin akan lokaci suka kwashi gawarsu zuwa asibitin cikin koyarwar jami’ar, kafin daga bisani aka sanar da mu abinda ya faru, kuma an yi jana’izarsu tun a ranar.”

A lokacin da Aminiya ta tuntubi Daraktan Hulda da Jama’a na jami’ar, Malam Auwal Ummar, ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ce, “a dan saurare mu domin muna kokarin shirya ziyartar iyayen yaran a hukumunce domin yi musu ta’aziya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here