Shirin kawo karshen yi wa mata kaciya nan da 2030

0
89

Kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da cewa, mata fiye da miliyan 200 a fadin duniya suka fuskanci yi masu kaciya abin da ake kira da ‘Female Genital Mutilation’ (FGM) a turance.

Rahoto ya nuna cewa a wannan shekarar ta 2023 akwai mata fiye da Miliyan 4.2 da ke fuskantar yiwuwar a yi masu kaciyar.

Haka kuma majalisar ta kiyasata cewa, katsewar zuwa makaranta da matsalar cutar korona ta haifar zai iya jefa wasu matan fiye da miliyan 2 suka fada komar masu yi wa mata kaciya a cikin shekaru masu zuwa in har ba a dauki kwakkwaran matakin da ya kamata ba.

Nijeriya ce kasa ta uku a duniya da ke tattare da mafi yawan mata a da aka taba yi wa kaciya, kamar yadda cibiyar majalisar dinkin duniya ta UNICEF ta bayyana a rahotonta. Hukumar ta kuma kara da cewa, yi wa mata kaciya yana kara karuwa a Nijeriya musamman ma a kan ‘yan mata masu shekaru 0 zuwa 14 a duniya. Abin takaicin kuma shi ne alkalumman sun tashi daga kashi 16.9 a shekarar 2013 zuwa kashi 19.2 a shekarar 2018, ‘‘Wannan abin damuwa ne matuka,”. UNICEF ta bayyana cewa, mata fiye miliyan 68 a fadin duniya suke fuskantar yiwuwar a yi masu kaciya a tsakanin shekarar 2015 zuwa shekarar 2030.

A shekarar 2012, babban zauren majalisar dinkin duniya (UNGA) ya bayyana ranar 6 ga watan Fabrairu na kowace shekara a mastayin ranar yekuwa da yaki da yi wa mata kaciya a duk fadi duniya, ranar da za a kara jaddada aniyar yaki da wannan mummunan al’adar da kokarin kawar da ita gaba daya.

Taken bikin wannan shekarar shi ne “Hada Hannu Da Maza da Matasa Don Kawo Karshen Yi Wa Mata Kaciya”. An kaddamar da shirin ne tare da hadin gwiwar UNFPA-UNICEF da hadadiyyar Kungiyar yaki da yi wa mata kaciya ta Duniya.

An kirkiro da shirin ne a shekarar 2022 don bada gudummawa ga al’ummar duniya don kawar da yi wa mata kaciya a fadinn duniya nan da shekarar 2030. Abin jin dadi a nan shi ne wannan shiri yana da alaka da tsarin cimma muradun karni mai lamba ta 5.3, wanda ke neman a daina kawo abubuwan da za su iya cutar da al’umma daga nan  zuwa shekarar 2030. Bangaren shirin ya bayar da karfi ne a kan kasashen da suka fi yawan wadanda ake ganin za a yi wa kaciyar a ‘yan shekaru masu zuwa.

Yi wa mata kaciya ya yi kamari a Nijeriya inda ake samun fiye da mata Miliyan 19.9 da aka yi wa kaciyar. Lamarin na Nijeriya yana kara samun wurin musammman ma tsakanin mata masu shekara 15 zuwa 49 amma ya yi kasa daga kashi 25 a shekarar 2013 zuwa kashi 20 a shekarar 2018, binciken ya kuma nuna yadda lamarin ya sake karuwa a tsakanin yara ‘yan shekara 0 zuwa 14 daga kashi 16.9 zuwa kashi 19.2 a daidai wannan lokacin da ake magana. An gano cewa kashi 86 na matan da aka yi wa kaciyar ana yi masu ne a tsakanin shekara 5 yayin da kashi 8 kuma an yi masu ne a tsakanin shekara 5 zuwa 14.

Tuni wakilin cibiyar majalisar dinkin duniya ta UNICEF a Nijeriya, Peter Hawkins ya bayyana cewa, yi wa mata kaciya bashi da wani tasiri a bangaren lafiya. Bayani daga kafafaen yada labarai ya nuna cewa, an yi wa mata kaciyar ne a yankin kudu maso yammancin kasar nan in da ake da kashi 35 yayin da kuma ake da karancin wadanda ake yi wa kaciyar a yankin Arewa maso gabas inda suke da kashi 6 kacal.

Jihohi biyar da aka fi yi wa mata kaciya a Nijeriya sune: Ebonyi, Ekiti, Imo, Osun da Oyo. Inda fiye da ‘yan mata da mata Miliyan 3 suka samu kansu da kaciya a tsakanin shekara 5 kamar yadda kididdiga ya nuna a shekarar 2022.

Ana yi wa matan kaciyar ne a mastayin karya dokokin hakkinsu na yara da mata kamar yadda dokokin kare hakkin yara ya nuna, haka kuma karyar hakkinsu ne na abin da ya shafi sirrinsu da kuma hakkinsu na kasancewa cikin ‘yanci, hanyoyin da ke bi wajen yi wa matan kaciya yana kai wa ga mutuwar wasu a sassan Nijeriya.

Bayani daga wani littafi da wata sharariyar mai fafuftukar yaki da yi wa mata kaciya mai suna Frances A. Althaus, ta sanar da yadda a shekarar 1984 suka yi taron a garin Dakar ta kasar Senegal, inda suka tattauana lamarin yi wa mata kaciya da sauran miyagun al’adu da ke cutar da rayuwar mata a sassan Afrika, daga nan suka kafa wata karkaffar kwamitin wanda zai yi aikin wayar da kan al’umma aka wannan mummuna al’ada.

An kuma bayyani a cikin littafin inda aka bayyana yadda kwamitin ya jagoranci kafa rassan kwamitoci a kasashe fiye 20 a sassan Afirika sun kuma bayar da gaggarumin gudumawa wajen yaki da wannan mummunar al’adar na yi wa mata kaciya, sun bayar da karfi a kan bayyana irin yadda yi wa mata kaciya yake cutar da rayuwar mata, an kuma samu babbar nasara a wannan yakin. Wanna gwagwamaryar ya haifar da wasu kananan kungiyoyi da suka yi fice a yakin da aka fuskanta na yi wa mata kaciya, sun kuma hada da ‘NOW’ a Nijeriya da kuma ‘Mandalaeo Ya Wanawake’ a kasar Kenya da ‘New Woman’ a kasar Egypt.

Littafin ya kuma fito da nasarar da aka samu a babban taro karo na 4 da aka yi a kasa Chana a shekarar 1995 inda aka samu nasarar ta yadda taron ya ayyana haramci ga wannan al’aada na yi wa mata kaciya a duniya, an kuma ayyana al’adar a matsayin tarzoma ga mata kuma karya hakkinsu ne.

Haka kuma bincike ya nuna cewa, ana wannan al’ada na yi wa mata kaciya a wasu kasase na yankin Asiya da latin Amurka abin takaici kuma shi ne wasu ‘yan gudun hijira dake zaune a yankin Turai ta Yamma, Arewacin Amurka da kasar Australia da New Zealand suna ci gaba da yi wa yaransu mata kaciya a boye.

A yayin da ranar Majalisar Dinkin Duniya ta ware na yaki da yi wa mata kaciya yake kara karatowa, a mastayinmu na jarida muna kara kira ga gwamantin tarayya ta gaggauta sanya ido a kan wuraren da ake samun rahoton karuwar yi wa mata kaciya, bai kamata a tilastawa kowa fadawa irin wannan mummunan al’adar ba. Yakamata a samar da wata karkarfar kwamiti domin fadakar da al’umma a kan bukatar kawo karshen wannan mummunan al’ada. Yakamata mu hada hannu mu fattaki al’adar yi wa mata kaciya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here