Sojojin kasashe na taimakawa wajen safarar miyagun makamai- MDD

0
123

Majalisar dinkin duniya ta ce akwai bukatar kasashen yankin Sahel su kara matsa kaimi ga yaki da kwararowar makamai a cikin al’umma wanda ta ce akasari makaman na gwamnatocin kasashen ne inda ta bukaci gudanar da bincike da nufin magance matsalar.

A wani rahoton da ta fitar a ranar talatar da ta gabata Ofishin majalisar dinkin duniya mai kula da magance matsalar yawaitar miyagun kwayoyi da tashe tashen hankula ya ce akasarin makaman da ke shiga hannayen ‘yan ta’adda a yankin Nahiyar Afrika na fita ne a tsakankanin kasashen.

Ofishin Majalisar dinkin Duniyar ya ce duk da cewar akwai ingantattun shaidun da ke tabbatar da kwararar makamai zuwa yankin na Sahel ta Sama daga kasashe kamar Faransa da Turkiyya ta mashigar kasar Najeriya ta bayyana a fili cewar akasarin makaman da ke shiga yankin na shiga ne daga yasu-ya su.

Majalisar dinkin Duniyar ta ce mafi yawancin makaman an karkatar da su ne daga rumbunan dana makamai na Sojin kasashen na yankin Sahel koma ta hanyar kamasu a fagen daga, ko Sata, ko kuma harin barayi.

 

Hakama inji majalisar dinkin Duniyar, mafi yawancin makaman da ake gani a hannun ‘yan ta’adda, suna zo masu ne daga tashin hankalin kasar Saliyo da Liberia, na baya-bayan nan kuwa,sun fito ne daga kasar libya.

Akan haka ne Majalisar dinkin Duniyar ke kira ga kasashen na yankin Sahel da su kaddamar da bincike su kuma yi abin da ya dace. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here