Yau kotun koli za ta soma sauraron kara kan wa’adin tsoffin kudi

0
144

A yau Laraba, 15 ga watan Fabrairu 2023, Kotun Kolin Najeriya za ta soma sauraron kara dangane da hukunci kan wa’adin amfani da tsofaffin takardun naira da aka sauyawa fasali.

Aminiya ta ruwaito cewa a Larabar makon jiya ce dai Kotun Kolin ta sahale a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudin har ya zuwa lokacin da za ta yanke hukunci.

Kotun Kolin dai ta yanke hukuncin na wucin-gadi bayan karar da wasu gwamnonin uku suka shigar a gabanta.

Gwamnonin Kaduna, Kogi da Zamfara ne dai suka garzaya kotun suna kalubalantar wa’adin tsofaffin kudin wanda Babban Bankin Najeriya CBN ya ce zai kare a ranar Juma’a, 10 ga watan Fabrairu.

Hakan ce ta sanya wasu alkalan kotun guda bakwai karkashin Mai Shari’a John Okoro, suka ce sun amince da bukatar gwamnonin uku na tsayar da matakin CBN na daina karbar tsohon kudin wanda bankin ya tsara zai fara aiki daga ranar 10 ga watan Fabrairu.

Sabon hukuncin dai na nufin an samu karin akalla kwanaki biyar a bangaren Kotun Kolin da ta tsara sauraron shari’ar a ranar 15 ga watan Fabrairu.

Ba a haka a kasashen da suka ci gaba —Tinubu

Wannan umarnin ya faranta wa bangaren jam’iyyar APC da dan takararta Bola Ahmed Tinubu da ya fitar da sanarwar lale marhabun da umarnin Kotun.

Tinubu ya bayyana farin cikinsa da matakin, yayin da yake cewa, Najeriya ta kama hanyar fadawa cikin rudani da rashin tabbas dangane da abin da ya shafi tattalin arzikin kasa da kuma siyasa sakamakon irin matakan da CBN ya dauka.

Tinubu ya ce kasashen da suka ci gaba kan bayar da wa’adin watanni 12 domin gudanar da irin wannan aiki na sauya kudin, yayin da ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su sake zama domin sake fasalin aikin ta yadda babu wani dan Najeriya da zai koka.

Shi ma Asusun Ba da Lamuni na Duniya IMF ya bukaci kara wa’adi ga jama’a domin ba su isasshen lokacin sauya kudaden nasu, yayin da yake cewa lokacin da CBN ya dauka ya yi kadan.

Matashiya

Tun da farko a ranar 31 ga watan Janairu CBN ya ce za a daina amfani da tsoffin takardun kudin naira 200, 500 da 1000.

Amma bayan korafe-korafe da aka yi ta yi, bankin ya kara kwanaki goma bayan sahalewar Shugaba Muhammadu Buhari.

Gabanin shigar da karar a kotu, gwamnonin jam’iyyar APC sun kai wa shugaba Buhari ziyara a fadarsa, inda suka nemi a kara wa’adin.

Ko da yake, ba su samu biyan bukata ba, amma Shugaban Kasar ya ce za a shawo kan matsalar karancin kudaden cikin kwanaki bakwai.

A halin da ake ciki, kotun ta ba bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudade a kasar umarni da su ci gaba da amfani da tsoffin kudaden har sai kotun ta yanke hukunci a zaman da za ta yi a ranar 15 ga watan Fabrairu.

Tun a watan Nuwambar bara, CBN ya soma fitar da sabbin kudaden da aka sauya wa fasali, sai dai karancin su ya jefa al’ummar kasar cikin halin ka-ka-ni-ka-yi.

’Yan Najeriya sun yi farin ciki

’Yan Najeriya sun jinjina wa Kotun Kolin saboda hukuncin da ta yanke na tilasta wa CBN yin watsi da wa’adin ranar 10 ga watan nan na dakatar da amfani da tsoffin kudaden da aka sauya wadanda karancinsu ya haifar da matsaloli baki daya.

Jama’ar kasar daga sassa daban-daban ciki har da talakawa da shugabanni da kuma malaman addinai sun bayyana korafinsu kan yadda aka samu matsala wajen sauyin, yayin da bankuna suka gaza samar da sabbin kudaden da ake bukata.

Wannan matsala ta sa aka fara samun bore a wasu biranen kasar da kuma kai hari a wasu bankuna, abin da ya kai ga rasa rai a birnin Abeokuta na Jihar Ogun.

Ko a birnin Ibadan, sai da ‘yan sanda suka tarwatsa gungun matasan da suka yi zanga-zanga domin nuna bacin ransu da karancin sabbin kudaden a bankuna, yayin da jama’a ke tururuwa domin neman su a bankuna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here