An mayar da kwalejin Sa’adatu Rimi da ke Kano matsayin jami’a

0
332

Gwamnatin Tarayya ta sahale wa Jihar Kano ta daga likafar Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kumbotso a zuwa matsayin jami’ar Jiha.

Babban Sakataren Hukumar Kula da Jami‘o’i ta Kasa (NUC), Farfesa Abubakar Rasheed ne ya bayyana hakan lokacin da yake gabatar da takardar shaidar ga Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.

Rasheed ya ce Jami’ar za ta taimaka wajen kara habaka bangaren ilimi a jihar, la’akari da takardun shaidar tsare-tsaren jami’ar da gwamnatin jihar ta gabatar wa NUC.

“Bisa cika ka’idojin zamowa jami’a da kwalejin ta yi, a madadin hukumar NUC, ina farin cikin sanar da ku cewa, daga ranar Talata, 14 ga watan Fabrairun 2023, ta tashi daga Kwalejin Ilimi ta koma Jami‘ar Jiha ta 61, kuma ta 221 a jami’o’in Najeriya baki daya,” in ji Farfesa Rasheed.

Ya kuma ce Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a (JAMB), da Asusun Tallafawa Jami’o’i (TETFUND), da ta Hukumar Kula da Matasa Masu yi wa Kasa Hidima (NYSC) sun samu ta su sanarwar a hukumance.

A nasa bangaren Gwamna Ganduje cewa ya yi jami’ar za ta fara aiki da fiye da lakcarori 116 da ke da takardun shaida matakin karatu na digiri na uku (PhD), da kuma guda 246 da ke matakin digiri na biyu (Masters).

“Baya ga haka kuma, shirye-shirye sun yi nisa na ganin an tsara kammala karatun daliban da ke yanzu haka ke karatu a ciki tana kwaleji, kafin zamowarta jami’a” in ji Gwamnan.

Ya kuma ce yunkurin na sa dori ne kan tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya fara, na samar wa jihar jami’o’i har biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here