Sarkin Zazzau ya nada hakimai 8

0
138

Masarautar Zazzau ta nada karin sabbin hakimai takwas tare da mika musu takardun fara aiki.

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ne ya kaddamar da sabbin hakiman a wani kwarya-kwaryan biki a fadarsa da ke birnin Zariya.

Sarkin Zazzau ya kuma mika wa sabbin hakiman takardunsu na aiki, wanda ya nuna nadin nasu sun fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Fabrairu, 2023.

An nada su ne bayan amincewar Gwmanan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ta hannun Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Masarautu ta jihar.

Sabbin Hakiman su ne:

  1. Alhaji Sufiyanu Umar Usman, Karfen Dawakin Zazza, Hakiman Pambegua.
  2. Mohammed Dahiru Dikko, Barde Kankanan Zazzau – Hakimim Pala.
  3. Haruna Abubakar Bamalli, Barde Kerrariyyan Zazzau – Hakimin Zangon Aya.
  4. Alhaji Kabiru Zubairu, Madaucin Arewan Zazzau – Hakimim Barnawa
  5. Dokta Bello Lawal, Durumin Zazzau – Hakimim Gubuchi respectively.
  6. Abdulkarim Zailani – Hakimim Sabon Birni
  7. Alhaji Auwalu Aliyu Damau – Hakimim Samu
  8. Alhaji Aminu Mohammed Ashiru – HakiminHunkuyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here