Tankar man fetur ta kama da wuta a gidan mai a Ilorin

0
118

Wata tankar man fetur makare da man fetur ta kama da wuta a yammacin ranar Asabar a wani gidan mai da ke Ilorin a jihar Kwara yayin da take sauke man fetur din, lamarin da ya haddasa mummunar gobara.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:05 na dare a gidan mai na M.M Rodiat Nigeria Ltd daura da asibitin Sobi Specialist Hospital Road-Ayegbami junction a karamar hukumar Ilorin ta gabas.

Duk da cewa ba a samu asarar rai ba a tashin gobarar, amma ta lalata dukiyoyin da sun haura Naira miliyan 50.

Mai ba gwamna shawara na musamman kan tsare-tsare, Saadu Salahu ya ce, ba don gwamnati da makwabta da manyan jami’an kashe gobara da jami’an tsaro sun kawo daukin gaggawa ba, da gobarar ta yi barnar da ba zata misaltu ba.

Daga bisani Gwamna Abdul Rahman Abdulrazaq ya ziyarci inda gobarar ta afku da misalin karfe 11:45 na dare domin duba halin da ake ciki. Gwamnan ya jajantawa wadanda abin ya shafa da mazauna yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here