Jami’an tsaro sun kama masu bangar siyasa kusan 100

0
104

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta sanar da kama matasa 93 bisa zargin su da bangar siyasa da tayar da zaune tsaye yayin da jam‘iyyu ke tarukan yakin neman zabe.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mamman Dauda ne ya tabbatar da kamen matasan ta cikin wata sanarwa da ya fitar mai dauke da sa hannun kakakain rundunar ‚yan sanda Abdullahi Haruna Kiyawa.

Kwamishinan ‘yan sandan ta cikin sanarwar yace an kama matasan ne bisa umarnin babban sufeton ‘yan sandan kasar Usman Alkali baba na kakkabe dukannin matasan da ke ikirarin daba a kasar baki daya.

A cewar sa an kama matasa ne a wani samame da ‘yan sandan suka kai filin taro na Sani Abacha da ke jihar lokacin da wata jam’iyya ke taron yakin neman zaben ta.

A cewar sa an kama matsan da bindigogi kirar gargajiya guda biyu, da wukake guda 32 da adda guda 1 sai kuma layoyi da guru masu tarin yawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here