An min tayin miliyan 150 da mota don na koma tafiyar Tinubu amma na ki — Sarkin waka

0
143

Fitaccen mawakin nan na masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Naziru Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin Waka, ya ce an masa tayin Naira miliyan 150 da tsaleliyar motar miliyan 80 don ya daina tafiyar Atiku ya koma tsagin Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC.

Sarkin Waka dai na daga cikin fitattun mawakan da suke goyon bayan takarar Atiku na jam’iyyar PDP a 2023.

Mawakin ya rera wa Atiku wata fitacciyar waka da ta shahara mai taken ‘APC sai mun ba ta wuta…’.

Cikin wata hira da ya yi da sashen Hausa na DW, Sarkin Waka ya ce ya ki amsar tayin da aka masa don komawa tafiyar Tinubu.

Mawakin ya ce yana da yakinin Atiku ya fi Tinubu cikakkiyar lafiyar da zai iya jagorancin kasar nan idan ya ci zaben ranar 25 ga watan nan da muke ciki.

Ya ce, “Na fi damuwa da bukatar kasa a kan bukata ra karan kaina.

“An yi min tayin miliyan 150 don na bar tafiyar Atiku da motar miliyan 80 don na koma tafiyar wani dan siyasa, amma na ki amincewa.

“Na ki amincewa ne saboda na san Atiku zai yi jagoranci mai nagarta a kasar nan fiye da halin da ake ciki a yanzu.

“Ta yaya zan goyi bayan takarar Tinubu bayan na san ba shi da lafiya? Addininmu ma ya mana nuni kan zabar shugaba mai lafiya, don yana cikin nagartar zaben shugaba,” in ji Naziru.

Sarkin Waka ba shi ne mutum na farko da ke goyon bayan dan takara a siyasa ba, da yawan ‘yan Kannywood suna shiga tafiyar siyasa.

Dauda Kahutu Rarara, mawaki ne da ya yi fice wajen yi wa APC waka tun daga 2015 zuwa yanzu.

Akwai ire-iren su Aminu Ala, Tijjani Gandu, sai kuma jarumai irin su Ali Nuhu, Abba El-Mustapha, Sani Danja, Yakubu Mohammed, Mustapha Naburaska da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here