Abun da zai sa na amince da shan kaye a 2023 – Kwankwaso

0
121

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa matakin da zai say a amince da zaben shugaban kasa da za a gudanar a wata mai kamawa shi ne, idan har an yi shi bisa tsari kuma ya yi rashin nasara zai amince ya rungumi kaddara.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a gaban ma’aikata da dalibai na jami’ar Abuja. Ya ce dole ne zaben 2023 ya kasance sahihin kuma karbabbe.

A cewar Kwankwaso, “Ban da matsala wajen amincewa da zabe idan har na yi rashin nasara. Amma kyakkyawan hanyar da zan amince da zaben 2023 shi ne, idan aka gudanar da sahihin zabe wanda ke kan tsari.”
Haka kuma ya sha alwashin kara yawan jami’an tsaron kasar nan a matsayin dubarar da zai dauka wajen kawo karshin rashin tsaro.

“Muna da kyakkyawan tsari a cikin manufofinmu kan yadda za mu shawo kan matsalar rashin tsaro a Nijeriya. Yau muna cikin takaici, inda a yanzu haka akwai mutane da dama da suka hada da maza da matsa an yi garkuwa da su.

“Za mu bai wa matasa maza da mata dama wajen hidamta wa kasa a matsayin jami’an tsaro, wadanda suka hada da sojoji, ‘yansanda, jami’an hukumar tsaro ta harin kaya (DSS) da dai sauransu,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here