Kwallon Osimhen na kama da ta Drogba – Mourinho

0
154

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Roma Jose Mourinho ya kamanta dan wasan gaban Napoli Bictor Osimhen da Didier Drogba, inda ya kara da cewa zai iya sayensa da a ce yana aiki da kungiyar da ke da kudi sosai.

Amma kuma Mourinho, dan asalin kasar Portugal ya gargadi dan wasan gaban na Nijeriya kan zuwa gasar Premier League ta kasar Ingila a irin salon wasan da yake yi.
Mourinho na magana ne a taron manema labarai, bayan kammala wasansu da Napoli, wanda suka yi rashin nasara 2-1 a filin was ana Maradona da ke birnin Naples a kasar ta Italiya.

”Osimhen kamar Drogba yake, amma Didier ba ya faduwa da gangan saboda haka na fada masa cewa ya ci kwallo mai kyau kuma akwai bukatar ya daina faduwa da gangan”, in ji Mourinho.

Mourinho ya ce kwallon da ya ci ta kayatar, domin ya taba cin irinta a farko haduwar su a wannan kaka, saboda haka dan wasa ne mai kyau sai dai dole ya daina faduwa da gangan.

Kungiyar kwallon kafa ta Napoli ce ke jan teburin Serie A da maki 53 a wasanni 20, kuma sau daya aka doke ta ta kuma yi canjaras biyu sannan ta bai wa Inter Milan da ke binta maki 13 wadda ke da maki 40, sai Lazio da Atalanta da AC Milan masu maki 38 kowannen su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here