Chanjin kudi: Farashin kayan abinci ya fadi warwas a kasuwannin Katsina

1
408

Farashin buhun dawa kudi kasa ya dawo naira dubu sha biyu N12,000, yayin da waken soya kudi kasa ya dawo N21,000 a kasuwar Talata ta Faskari.

Kasuwar garin Faskari, jihar Katsina dake ci duk irin wannan rana ta Talata, farashin buhunan hatsi ya fadi kasa warwas sakamakon babu garin kudade a hannun yan kasuwa da masu saye.

Hakan ya sa farashin buhun kayan hatsi na abinci ya dare zuwa gida biyu a kasuwar, inda farashin sayen buhuna ga mai bukatar a yi masa taransifar banki ya fi yin sama, a inda farashin kudin buhunan ga mai son kudi kasa ya fadi kasa warwas sakamakon babu garin kudaden a hannun yan kasuwar da suka zo cin kasuwar a yau.

A wasu buhunan ana samun rangwamen har kusan dubu shida ga duk buhu daya, ga wanda yake son a saya a biya shi da garin kudi.

Misali an sayar da

Buhun waken soya a kan farashin naira dubu ashirin da bakwai N27,000 ga wanda ya aminta a yi masa taransifar banki, ga wanda kuma yake son a saya a biya shi da kudi kasa ana sayen duk buhu daya a kan naira dubu ashirin da daya N21,000 ko a haka ma akwai waÉ—anda suka mayar da kayansu gida saboda suna bukatar garin kudin kuma babu su a hannun yan kasuwar kuma babu kudin a wurin masu sana’ar POS, kamar yadda DPO na kungiyar masu sayar da hatsi na karamar hukumar ya tabbatar man, bayan kuma ni da kaina na ga yadda kasuwar ta kansace.

 

A takaice dai ga yadda farashin buhunan hatsin ya kasance a yau Talata;

Buhun Waken soya taransifa N27,000, kudi kasa N21,000

Buhun dawa taransifa N15,000, kudi kasa N11,000 zuwa N12,000

Buhun Masara taransifa N17,000, kudi hannu N14,000

Buhun Dauro N20,000

Farin wake taransifa N27,000, kudi hannu N24,000

Katsina Post

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here